‘Yan Takarar Shugaban Kasa A Aljeriya Sun Nuna Rashin Amincewarsu Da Sakamakon Zaben Kasar

Dukkan ‘yan takarar shugaban kasa sun ki amincewa da sakamakon zaben kasar Aljeriya A wani matsayi da ba a taba ganin irinsa ba, ‘yan takara

Dukkan ‘yan takarar shugaban kasa sun ki amincewa da sakamakon zaben kasar Aljeriya

A wani matsayi da ba a taba ganin irinsa ba, ‘yan takara uku na zaben shugaban kasa a Aljeriya, Abdul-Madjid Tebboune (wanda ya lashe zaben kashi 94 cikin dari), da Abdul-A’li Hassani Sharif, da kuma Youssef Aoushish, a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar sun bayyana rashin amincewarsu da sakamakon farko da shugaban hukumar zaben kasar ya sanar Mohammed Sharfi.

Da misalin karfe sha daya na dare ne aka fitar da sanarwar hadin gwiwa, mai dauke da sa hannun jami’an daraktocin yakin neman zabe na ‘yan takarar shugaban kasar uku, inda a ciki har da daraktan yakin neman zaben dan takarar da wa’adin mulkinsa ya kare Abdul-Madjid Tebboune, wanda da farko da dama ba su yi imani yana cikin masu sukan ba sakamakon mamakin yadda shugaban da ya yi nasara da gagarumin rinjaye zai zama cikin masu sukar sakamakon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments