Habasha ta zargi Masar da kokari ci gaba da yin ikirarin mallakar kogin Nilu yayin da zaman ɗar-ɗar ke daɗa ƙaruwa tsakanin ƙasashen biyu.
Cikin wata wasiƙa da ta aike wa kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, Habasha ta ce ta yi fatali da abin da ta kira jerin zarge-zarge marasa tushe da Masar ta yi game da takaddamar da ta shafi wata madatsar ruwa mai cike da cece-kuce da Habasha ta shafe shekara 13 tana gina wa a kogin Nilu.
An kusa kammala ginin madatsar ruwan kuma tuni ta soma samar da hasken wutar lantarki.
Wannan takaddamar baya bayan nan zuwa ne a daidai lokacin da Masar ta kulla huldar soji da makwabciyarta Somalia, wadda ita ma ke da nata rashin jituwar da Habasha.
Rikicin ya samo asali ne tun a shekara ta 2011 lokacin da Habasha ta fara gina babban madatsar ruwa ta ‘Gerd’ a kan kogin Blue Nile, inda kashi 85% na ruwan Nilu ke kwarara.
Masar, tare da Sudan – wanda ita ma kogin Nilu ke bi ta cikinta, na ƙara nuna fargabar cewa za a iya fuskantar barazana ga hanyoyin samar da ruwan da suke bukata, musamman idan aka samu fari na shekaru a jere.