Grossi: IAEA a shirye take ta shiga tattauna tare da Iran nan gaba kadan

Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya ce yana fatan kafa wata tattaunawa mai ma’ana nan ba da jimawa ba

Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya ce yana fatan kafa wata tattaunawa mai ma’ana nan ba da jimawa ba tare da shugaban Iran Masoud Pezeshkian don samar da “sakamako mai kyau.”

“Bayan zaben da aka yi a Iran (a watan Yuli), na yi magana da shugaban kasar Pezeshkian, inda muka jaddada muhimamncin  sake bude tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin hukumar IAEA da gwamnatin Iran,” in ji Grossi a cikin jawabinsa na farko ga taron na shekara-shekara, na Hukumar IAEA a Vienna a ranar Litinin.

Ya kara da cewa sabon shugaban na Iran ya amince da ganawa da shi “a daidai lokacin da ya dace”.

Shugaban hukumar Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce: “Ina karfafawa kan muhimamncin gudanar da irin wannan taro nan gaba kadan, ta yadda za mu iya kafa tattaunawa mai ma’ana da za ta kai ga samun sakamako na gaske kuma mai nagarta.”

A cikin watan Yuni ne hukumar ta IAEA ta zartas da wani kuduri kan Iran duk da gargadin da Tehran ta yi na cewa za ta mayar da martani ga wannan matakin.

A watan Nuwamba, Iran ta fara inganta sinadarin Uranium zuwa kashi 60% a cibiyar samar da makamashin nukiliya ta Fordow, bayan sanar da hukumar ta IAEA matakin da ta dauka a wata wasika.

Har ila yau Iran ta sanya sabbin na’urorin IR2M da IR4 a cibiyar Natanz, wadanda a yanzu ayyukansu sun yi nisa wajen tace sanadarin uranium.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments