MDD Ta Yi Martani Kan Hare-Haren Isra’ila A Yammacin Kogin Jordan

A cikin wata sanarwa ta MDD, manyan ayyukan soja da Isra’ila ke yi a Gabar Yamma da kogin Jordan da ta mamaye suna kara  ta’azzara

A cikin wata sanarwa ta MDD, manyan ayyukan soja da Isra’ila ke yi a Gabar Yamma da kogin Jordan da ta mamaye suna kara  ta’azzara al’amura a yankin da dama tuni yake ciki “mawuyacin” yanayi, wanda ya ƙara ta’azzara irin ta’annatin da ‘yan kama-wuri-zauna ke yi.

Da yake bude wani taro na Hukumar Kula da Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, Volker Turk ya koka kan yadda ake Kara aikata ta’annati a Gaɓar Yamma, a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai manyan hare-hare.

“A Gabar Yamma, mummunan ayyukan da ake yi, wasu a wani irin mataki da ba a taɓa gainin irinsa ba a cikin shekaru 20, suna ta’azzara yanayin da ake ciki, wanda dama tuni ya tabarbare, saboda ta’annatin da ‘yan kam-wuri-zauna suke yi, kamar yadda Turk ya shaida wa Majalisar.

Akalla karin wasu Falasdinawa 16 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu tun daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa 40,988, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da yaki ya daidaita.

Sanarwar ma’aikatar ta kara da cewa wasu mutane 94,825 sun samu raunuka a harin.

“Sojojin Isra’ila sun kashe mutane 16 tare da raunata wasu 64 a wasu ‘kisan gilla’ biyu da suka yi wa wasu iyalai a cikin sa’o’i 24 da suka gabata,” in ji ma’aikatar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments