Shugaban hukumar kwastam ta Iran Mohammad Rezvanifar ya bayyana cewa, cinikin da ba na man fetur da Iran ke yi da kasashen kungiyar OIC ya karu da kashi 15% zuwa dala biliyan 26.7 a watanni biyar na farkon wannan shekara.
M. Rezvanifar ya kara da cewa, yawan cinikin da ba na man fetur ba tsakanin Iran da kasashe mambobin kungiyar OIC a wannan lokaci ya kai tan miliyan 42.3, inda ya karu da kashi 10% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Ya ci gaba da cewa, daga cikin jimillar cinikin man fetur tsakanin Iran da kasashe mambobin kungiyar OIC 56, an ware tan miliyan 33.6 da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 13.5 don fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare.
Ya kuma kara da cewa, a cikin wannan lokaci, an shigo da ton miliyan 8.7 na kayayyaki da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 13.2 daga kasashe mambobin kungiyar OIC, wanda hakan ya karu da kashi 18 cikin 100.
A cewar Rezvanifar, mafi girman cinikin da ba na man fetur ba tsakanin Iran da kasashe mambobin kungiyar OIC a cikin watanni biyar na farkon wannan shekara ya kasance tare da UAE, Turkiyya, Iraki, Pakistan, da Oman, wanda ya kai na dalar Amurka biliyan 24.