Gwamnatin Burkina Faso Ta Cire Tambarin ECOWAS A Kan Passport Da Take Bawa Yan Kasar

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta fara bada passport ga mutanen kasar ba tare da tambari ko sunan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta fara bada passport ga mutanen kasar ba tare da tambari ko sunan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ba.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasashe 3 na yankin Sahel, Burkina Faso, Mali da kuma Nijer sun dage kan matsayinsu na ficewa daga kungiyar ECOWAS .

Labarin ya kara da cewa, wani Jami’an hukumar bada passport na kasar Burkina Faso ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa a cikin sabbin Passport da suke bayarwa a halin yanzu babu sunan ECOWAS a cikinsa kuma babu inda aka ambaceta.

A shekarar da ta gabata ce kasashen uku na sahel, wadanda sojoji suka yi juyin mulki a cikinsu, suka balle daga kungiyar mai kasashen 15 na yammacin Afirka wanda kuma an kafa ta fiye da shekaru 50 da suka gabata. Tare da kafa wata kawance ta kasashen Sahel.

Banda haka kasashen uku sun juyawa kasashen yamma baya, sun kuma koma ga kasshen gabas musamman kasar Rasha don tabbatar da tsaro a cikin kasashen nasu. Kasashen suna zargin kasashen yamma da tatsar arzikin kasashensu, da kuma haddasa matsalolin tsaro a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments