Iran Ta Bayyana Rashin Lamuntar Duk Wata Barazana Ga Kasashen Da Take Makwabtaka Da Su

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ba za ta taba lamuntar keta hakkin kowace kasa daga cikin makwabtanta ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ba za ta taba lamuntar keta hakkin kowace kasa daga cikin makwabtanta ba

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Duk wata barazana ga amincin kasashen da suke makwabtaka da Iran ko kuma mamaye wani yankinta, lamari ne da Iran ba za ta taba lamunta ba.

Ministan harkokin wajen Iran ya wallafa wani sako a dandalin sada zumunta na yanar gizo cewa: Aminci da tsaro gami da zaman lafiyan yanki, ba sune kawai masu muhimmanci ga Iran ba, saboda daya daga cikin muhimman jigogin amincin kasar Iran akwai rashin aminta da duk wani matakin yin barazana ga wata kasa da take makwabtaka da ita, ko barazana ga kan iyakokinta shin a shiyar arewa ne ko kudanci ko gabashi ko kuma yammaci, duk matakai ne da ba za ta taba lamunta ba, kuma tana daukansa a matsayin jan layi ga tsaron kasarta.

Abin lura shi ne cewa: Araqchi yana nuni ne da kan iyakar Iran da Armeniya da kuma matsayin Iran kan mashigar “Zangeh Zor” da kasashen Azabaijan da Turkiyya suka dage wajen samar da ita, kuma da alama akwai goyon bayan kasar Rasha, yayin da Iran take kin amincewa da hakan sosai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments