A wasan mutsa jiki a gasar ‘2024 Paris Paralimpic’ wanda ke gudana a birnin Paris na kasar Faransa a halin yanzu. Wani dan kasar Iran mai jefa sandar Javelin mai suna Sa’ed Afrooz ya sami lamabar zinari inda ya zo na daya a gasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa Afrooz ya fuskanci yan wasan Javelin na kasashen China, Colombia 2, Morocco, Brazil da kuma Iraki a filin wasannin na birnin Paris inda ya lallasasu gaba daya ya kuma karbi lambar zinari a wannan wasan.
Banda haka Afrooz ya wuce nisan da aka saba a wasannin Paralympic na duniya inda ya jefa sandar Javelin samfurin F34 zuwa nisan mita 40.18, da mita 40.67 da kuma 41.16. wanda ya wuce na wadanda aka yi a bayan. Daga karsgen Afrooz ya zama zakara tare da jefa sandar Javelin zuwa nisan mit 41.16.