Tallafin Da Kasashen Yamma Suke Bawa HKI A Yakin Gaza Ya Na Komawa Kansu

Tallafin da ba iyakan da kasashen yamma suke bawa HKI a yakin da take fafatawa a Gaza, ya bunkasa kasashen da suke gwagwarmaya da ita

Tallafin da ba iyakan da kasashen yamma suke bawa HKI a yakin da take fafatawa a Gaza, ya bunkasa kasashen da suke gwagwarmaya da ita a yankin kudancin Asia.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakal Amal Saad wani malamin jami’a kuma mai sharhi kan al-amuran gabas ta tsakiya yana fadar haka a shafinsa na X  ya kuma kara da cewa: tallafin da kasashen yamma gaba daya suke bawa HKI ya zama abin zargi da kunya ga kasashen idan suna da kunyar.

Saad ya kammala da cewa, in da taimakon wadannan kasashen yamma sun taimakawa HKI, da kuwa ta kare da gaza. Amma duk tare da tallafin makaman da kayakin yakin da suke bawa HKI, ta kasa cimma burinta na ganin bayan kungiyar Hamas, har ila yau tallafin bai kai ga maida fursinoninta da ke hannnun Hamas ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments