Najeriya: Tashin Farashin Man Fetur Ya Sa Kuden Hayarsu Ya Karu Da kasha 50% A Duk Fadin Kasar

Saboda sanarwan da kamfanin NNPC Ya bayar na kara farashin man fetur a gidajen man kanfanin da suke fadin tarayyar Najeriya kasar ya sa farashin

Saboda sanarwan da kamfanin NNPC Ya bayar na kara farashin man fetur a gidajen man kanfanin da suke fadin tarayyar Najeriya kasar ya sa farashin ababen hawa a kasar ya tashi da kashi 50% a duk fadin kasar.

Jaridar Daily trust ta bayyana cewa kamfanin NNPC ta sanya sabon farashin man daga Naira 855 zuwa 897 a gidajen mata a duk fadin kasar dai dai nisan inda gidan man yake daga Lagos. Sannan kamfanoni masu zaman kansu sun kara farashin man zuwa naira 930 zuwa 1200. Tashin farshin ya sa mutane cikin wahalhalu da dama inda wasu suke takawa da kafa zuwa wurare masu nisa, wasu kuma sun kasa zuwa aiki saboda tsadar ababen hawa.

Kungiyoyi da dama sun nuna rashin amincewarsu da karin farashin man, sannan sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayyar ta dawo da farshin man kamar yadda yake.

Jam’iyyar PDP mai adawa da kungiyar Afenefere ta yorobawa da kuma kungiyar kwadago duk sun bukaci a maida farashin man kamar yadda yake a da.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments