UNICEF : Rigakafin Polio A Gaza Na Daya Daga Cikin Kamfe Mafi Hatsari A Duniya

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce ko da an dakatar da wani bangare na tashin hankali a Gaza, allurar

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce ko da an dakatar da wani bangare na tashin hankali a Gaza, allurar rigakafin cutar shan inna ga yaran Falasdinawa na daya daga cikin kamfe mafi wahala da hadari a duniya.

Hukumar ta bayyana cewa sama da tawagogi 500 ne aka tura a tsakiyar Gaza a wannan makon, inda suke ba da rigakafin ga yara ‘yan kasa da shekaru 10.

A cewar asusun na UNICEF, an yi wa yara kimanin 189,000, wannnan riga kafin wanda ya zarce abin da aka yi tsammani.

Duk da haka, ta ce, “Wannan yana daga cikin kamfe mafi hadari a duniya.”

Ta ce Gaza, wanda yakin Isra’ila ya lalata na tsawon watanni 11, ya riga ya zama wuri mafi hatsari a duniya don zama ga wani yaro, kuma ko da an dakatar da cutar Polio, yakin rigakafin yana fuskantar babban hadari da cikas da ba za a iya kwatantawa ba, ciki har da lalacewar hanyoyi da sha’anin kiwon lafiya.

A Ranar Laraba ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kuma sanar da kammala aikin rigakafinta a tsakiyar Gaza, inda za’a karkata aikin zuwa yankunan kudanci da arewacin Gaza.

Shugaban hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya yaba da babban ci gaba da ake samu a yakin allurar rigakafin, amma ya ce ana bukatar tsagaita bude wuta na dindindin domin sassauta wahalhalun jin kai a Gaza.

Wannan gagarumin gangamin rigakafin ya biyo bayan gano cutar shan inna ga wani jariri a watan da ya gabata, wanda shi ne na farko a zirin Gaza tsawon shekaru 25.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce barnar da Isra’ila ta yi wa fannin kiwon lafiya da tsaftar muhalli ne ya haifar da barkewar cutar mai saurin kisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments