Sojojin Yemen Sun Kai Farmaki Kan Jirgin Ruwa Mai Suna GROTON A Tekun Aden

Sojojin ruwa na kasar Yemen sun yi luguden wuta kan wani jirgin ruwan daukar kaya mai suna GROTON a cikin Tekun Aden bayan da kamfanin

Sojojin ruwa na kasar Yemen sun yi luguden wuta kan wani jirgin ruwan daukar kaya mai suna GROTON a cikin Tekun Aden bayan da kamfanin jirgin ya sabawa dokar kasar ta Yemen na hana dukkan jiragen kasuwanci masu zuwa HKI ko mallakin Amurka da Burtania wucewa ta wadannan hanyoyi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Yahyah Saree kakakin sojojin na Yemen yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa sojojin sun yi amfani da jiragen yaki samfurin UAV da kuma makamai masu linzami don kai wadannan hare hare wadanda suka sami jirgin kamar yadda aka tsara.

Gwamnatin kasar yemen dai ta tabbatar da dokarta a tekun Maliya da Tekun Aden da kuma Tekun Indiya na hana jiragen ruwan kasuwanci ratsawa ta cikinsu har zuwa lokacinda HKI zata kawo karshen yakin da take yi  a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments