Namibiya Ta Hana Wani Jirgin Ruwa Dauke Kayan Yaki Wucewa Yankunan Falasdinawa Da Aka Mamaye

Kasar Namibiya ta hana wani jirgin ruwa dauke da ake kyautata zaton yana dauke da kayan yaki da ya nufi yankunan Falasdinawa da aka mamaye

Kasar Namibiya ta hana wani jirgin ruwa dauke da ake kyautata zaton yana dauke da kayan yaki da ya nufi yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya tsaya a tashoshin ruwanta bayan da ta yi zargin cewa za a yi amfani da kayayyakin da jirgin ke dauke da a yakin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza.

Jirgin ruwan MV Kathrin mai tutar Portugal ya nemi izinin shiga tashar ruwa ta Walvis Bay ta kasar ne ranar Litinin, saidai hukumomin kasar sun haramta mas ahakan

Da take tsokaci game da lamarin, ministar shari’a ta Namibia, Yvonne Dausab ta ce, “Bayan samun rahoton cewa jirgin ruwan na dauke makamai da aka yi niyya” shigar dasu ga yankunan da aka mamaye, na Falasdinawa ta tuntubi hukumomin da abin ya shafa” ciki har da batun yarjejeniyar kisan kare dangi.

Ta ce binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa lallai jirgin yana dauke da ababen fashewa da aka nufi yankunan.

Ministar ta kara da cewa, “Namibiya ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu na kar ta ba da goyon baya ko kuma ta hada kai a laifukan yaki na Isra’ila, laifukan cin zarafin bil’adama, kisan kare dangi, da kuma mamayar da ta yi wa Falasdinu ba bisa ka’ida ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments