Kissoshin Rayuwa Na 35: Kissar Fatimah Azzahar (s) Diyar Manzon Allah (s)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa. Shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa. Shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin ‘Dastane Rastan’ na Shahid Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin mathanwai na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma dai ciki wasu liattafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahar (s) diyar manzon All..(s) kuma mahaifiyar Alhassan da Alhussan (a) da muke kawo maku, mun tsaya inda muka yi magana dangane da yawan ilminta (s), da kuma hadisai daga manzon All…(s) inda yake cewa da Aliyu da Fatima da yayansu ne taskar ilmi a cikin al-ummarsa, sannan duk wanda ya nemi shiriya daga wajensu zai samu. Mun ji yadda wata mata ta zo ta dauki ilmi a wajenta har sau 10, daga nan ta ji kunyar ta sake dawowa, amma Zahra (s) ta ce mata All..ya dauki jingarsu na su watsa ilmi tare da lada wanda yawanta ya fi abinda zai cika kasa har zuwa Al-Arshi na lulu’i.

Har zuwa inda take cewa babanta (s) ya fada mata cewa zaren aljanna ya fi daraja a kan duk abinda rana da haska a kansa a nan duniya.

Da kuma inda take cewa menen amfanin mai azumi wanda baya bayan kiyaye harshensa, da jinsa da ganisa da kuma gabbansa?.

A ci gaba da kawo maku hadisan da aka karbo daga Zahra(s) a yau zamu fara da hadisin, shahida Zaidu dan Aliyu dan Hussain (s) daga iyayensa (s) daga Fatima (s) ta ce: naji manzon All..(s) yana cewa: Lalle a ranar jumma’a akwai wani lokaci, mutum musulmi ba zai yi muwafaka da shi yana rokon All..mai girma da daukaka ba face ya biya masa bukatarsa.

A wanim hadisin tana cewa nace: Ya manzon All..(s) wani lokaci ne wannan? Sai ya ce: Idan rabin kwallon rana ya kusan bacewa. Sai yace: Fatimah (s) tana fadawa mai khidimarta, ki hau kan gini, idan kinga rabin kwallon rana ya kusan bacewa ki fada mani in yi addu’a.

Ankarbo hadisi, daga Hassan dan Alhassan daga mahaifiyarta Fatimah (s) tace: Manzon All..(s) yace: Duk wanda ya kwana da romon nama a hannunsa kada ya zargi wani bisa duk abinda ya same shi.

Anan yana nufin idan mutum ya ci abinci musamman nama bai wanke hannunsa daga romon abicnin ba, ko naman ba, to dabbobi suna iya zuwa wajensa yana barci su cutar da shi saboda kanshin naman da suke ji yana tashi daga hannunsa.

A wani hadisin daga Hassan daga babansa, daga Fatima (s) tace: Manzon All..(s) yana cewa ‘rundunoni biyu azzalumai idan suna yaki a tsakaninsu, All..zai kyalesu, ba zai damu da wanda ya yi galaba a kan wani ba, kuma rundunoni azzalumai biyu ba zasu kara ba, face duk musibun da suka jawo su zata shafa.

A wani hadisin daga Fatima diyar Alhussain (s) daga Fatimah (s) diyar manzon All..(s) tace: Manzon All..(s) yace: dukkan yan adam ana jinginasu da iyayensu daga hahaifinsu, sai yayan Fatima, to Lalle nine babansu, da kuma wanda ake jinginasu da shi.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin hadisan da aka karbo daga Fatima diyar manzon All..(s). Amma a halin yanzu zamu ci gaba da kawo maku hidisin Allow, kamar yadda zaku ji.

Ya zo cikin littafin Kafi, daga Abu basir daga baban Abdullahi (Imam Sadik(a) yana cewa: babana (Imam Bakir (a)- yace wa Jabir dan Abdullahil ansari : Ina son kebewa da kai, a duk lokacinda ayyukanka suka yi sauki, ina son kebewa da kai in tambayeka dangane da ita. Sai Jabir ya ce masa, duk lokacinda kake bukata.

Sai suke kebe watarana, sai yace masa: Ya Jabir, ka bani labarin allon da ka gani a hannun mahaifiyata Fatimah (s), diyar manzon All..(s), kuma menene mahaifiyata Fatimah ta fada maka abinda yake rubuce a cikin allon?.

Sai Jabir Yace: Na rantse da All..na shiga wajen mahaifiyarka Fatimah (s) a lokacin rayuwar manzon All..(s), na yi mata barka da haihuwar Alhussain (a), sai na ga wani allo kore a hannunta, na yi zaton dutsen Zamarradu ne kore, sai naga farin rubutu a cikinsa, kamar launin rana, sai nace mata: Iyaye na fansarki, ya ki diyar manzon All..(s) menen wannan allon.?

Sai tace: wannan alone, All..ya bada shi kyauta ga manzonsa (s) a cikinsa akwai sunan babana, da sunan majina, da sunan yayana biyu, da sunan wasiyay daga yayana, babana ya bani shi don yayi mani bushara da shi.

Sai Jabir yace: sai mahaifiyarka Fatimah(s) ta bani shi, sai na karanta shi, sai na rubuta shi, sai babana Imam Bakir (s) ya fadawa Jabir, shin kana iya nuna mani shi? Sai yace: Kwarai kuwa.

Sai mahaifina ya tafi da shi zuwa gidan Jabir, sai ya fito masa da wata takardan fata.

Sai ya ce: Ya Jabir, ka duba cikin takardanka, ni kuma zan karanta maka abinda ke cikinta. Sai Jabir ya duba a cikin takardansa, sai mahaifina ya karantata, bai sabawa abinda yake cikin takardan ko da harafi guda ba. Sai Jabir Yace: Na rantse da All..haka na ganshi a cikin allo a rubuce. Ga mataninsa kamar haka.

Da sunan All…Mai Rahama Mai Jinkai

Wannan takardan daga All..mai girma da daukaka, ga Muhammadu annabinsa, kuma haskensa, kuma jakadansa, kuma hijabinsa mai kuma shiryatarwarsa, amintaccen Ruhi ya sauko da shi daga wajen Ubangijin Talikai. Ka daukaka sunayena ya Muhammadu, ka kuma gode mani saboda nimomi na, kuma kada ka musanta falalata, lalle ni ne All…, Babu abinda bauta da gaskiya sai ni, mai shafe azzalumai, mai sauyawa wadanda aka zalunta, mai hukunci a ranar lahira, lalle nine All…babu wani abin bauta da gaskiya sai ni, to duk wanda ya kaunaci wani abu banda falalata, ko kuma ya ji tsoro banda adalci na, zan azabtar da shi, azaba wacce ba zan azabtar da wani da irinta ba daga cikin talikai.

Ka bauta mani ni kadai, kuma kayi tawakkuli a gareni, Lalle ban taba aiko da annabi, kuma na cika masa kwanakinsa a duniya ba, sannan tsawon kwanakinsa sun kare ba, sai na sa masa wasiyyi. Kuma lalle ni na fifitaka a kan annabawa, kuma na fifita wasiyinka a kan sauran wasiyyai, kuma na girmamaka da yayanka biyu, kuma jikokinka, Hassan da Hussain.

Sai na sanya Hassan taskar ilmina, bayan karewar kwanakin mahaifinsa,. Kuma na sanya Hussain Taskar wahayi na, na kuma daukakashi da shahada, na kuma cika masa da nasara, shi ne mafificin wanda ya taba yin shahada.  Kuma mafi daraja daga cikin shahidai, kuma na sanya cikekken kalmata tare da shi, da kuma kololuwar hujjata a wajensa, ina bada lada kuma in azabtar, tare da yayansa, na farkonsu, Aliyu shugaban masu bauta, kuma kawar waliyan da suka shude, da dansa mai kamada kakansa Mahammadu, Muhammadu mai tsaga ilmina, kuma ma’ajiya ko taskar hikimata, Sannan wadanda suke kokwanta a cikin Jaafaru da sannu zasu halaka, musantashi musantani ne, zancen gaskiya daga wajena, itace, Lalle zan daukaka makomar Jaafaru, kuma zan faranta masa rai cikin mabiyansa, da masu taimaka masa, da kuma majibantansa.

Na zabi Musa bayansa, Fatina mai tsananin duhu, zata bullo a zamaninsa, don zarin wajibai na baya yankewa, kuma hujjata bata boyewa, kuma lalle ne masoyana za’a shayar da su da cikekken kofi, wanda ya musanta daya daga cikinsu ya kafircewa ni’imata, kuma wanda ya sauya aya guda daga cikin littafinsa, to hakika ya yi mani karya, azaba ta tabbata ga makaryata, masu musantawa. A lokacin karewar raruwar Musa bawana kuma masoyi na, to kuma zabena yana cikin Aliyu waliyyi na, mataimaki wanda kuma zan sanya nauyin ilmin annabci a kansa, kuma zan jarrabe shi da nauyin shugabanci, wani dan sharri mai girman kai ne zai kashe shi, sannan za’a binneshi a garinda bawa na gari ya gina a kusa da mafi sharrin halittu..

Masu sauraro saboda kurewar lokaci a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All…ya yarda zamu dora daga inda muka tsaya. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments