Madagaska : Shugaba Rajaolina ya ce ‘’ana zanga-zanga ne da nufin tsige shi “

Shugaban Madagaska Andry Rajoelina ya bayyana cewa gagarumar zanga-zangar da akeyi a kasar, na da nufin “yi masa juyin mulki,” ne. A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Rajaolina, ya yi ikirarin cewa matasan da suka yi gangami a kan tituna, da tun farko suke yin Allah-wadai da katsewar wutar lantarki […]