Wane ne ake cema Yaro? | SHAFI’U & Shaikh Anas Abdullah

Share

Kalmar tarbiyya, ararriyar kalma ce daga Larabci (التربية aka Hausantar da ita. Kalma ce magamaiya, wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta renon jikin yaro; hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa, tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a, a al’ummance da kuma ɗaiɗaiku.