Tsufa Abubuwan dake biyo bayan sa | NAFISA & MARYAM

Share

Anan Malama Tayi iyakan ƙoƙarin domin fayyacewa masu kallo Abubuwa kamar haka:
1- Menene cikakken Ma’anar Tsufa a wanne lokaci ne na rayuwar mutum ake kiran lokacin da lokacin da Mutum ya tsufa?
2- Sannan ya ya Mutum zai yi domin fara shiryawa tsufar tun kafin gabatowar shi domin ya zamto tsufar tashi tazo da sauki da kuma rashin Cututtuka kamar yanda wasu ke fuskantar hakan sakamakon rashin shirin da basu yiwa tsufar ba, sai kawo lokacin da ya riske su sai su farka daga nannauyar barcin gafalar da suke ciki.
3- Sannan Mlm ta sanar da Hanyoyin da Mutum zai shiryawa tsufar kafin zuwan lokacin ta yanda zai zamto bai shammaci Mutum ba, kuma bai yi fargar jaji ba ta yanda da na sanin da zai yi bazai yi masa amfani ba ko kaɗan.