AIMAKON WANDA AKE ZALUNTA. Na Farko Zamu so muyi mukaddima na cewa Addinin Musulunci yana da fadi Kuma Yana da zurfi ta yanda Dukkanin wanda ya shaida da la’ilaha illallah Muhammadur Rasulullah to a wurin mu da wurin addininmu Musulmi ne Kuma ɗan uwanmu ne, Yana da hakki akan mu kamar yanda kowanne ɗan uwanmu musulmi da muka hadu a wannan addinin na Musulunci. Abu na biyu Wannan Addinin namu na Musulunci kai Bama kaɗai wannan Addinin namu na Musulunci ba Dukkanin wani wanda ke da ɗan adamtaka ya san munin Zalunci da aikata shi a gefe , sannan hankali ya hukunta kyau da dacewar taimakon wanda ake zaluntar.