BADA AMSA KAN YAWAN TAMBAYOYIN DA YARA KE YI. Tabbataccen abu ne cewa cikin marhalolin da yaro ke wuce su shine Marhalar da akan samu wasu daga cikin yaran basu jin Magana. To Yanzu nade hannu kawai zamu yi saboda yaro baya jin Magana mu ce mu yafi karfin mu saboda haka babu yanda zamu yi dashi? Ko kuwa a’a hanyace zamu dauka da duka da kushuna da bada tsoro da sauran su domin gabashi wannan rashin jin Maganar? Wannan shine Abin da mai jawabin ya kawo mana hanyar magance wannan lamarin. Kuma hanyoyi ne da Addini ya tabbatar dasu haka kuma ilmin sanin halayyar dan Adam suma sun taimaka wurin karfafan hakan. Wanda kuma matuƙar mahaifa sun yi kamar yanda Malam ya kawo tabbas zamu kai ga kyakkyawar natija magance wannan rashin jin Maganar.