Kalmar adalci kalma ce mai dadin fadi, kuma kalma ce da duk wani dan adam idan ya fade ta yakan ji dadi kuma ya ji dadin a aikata masa ko shima ya aikatawa wani.
Sai dai kalmace ce kuma da idan a fito duniyar waje wurin da ake bukatar aikata ta wasu da dama aikatatan kan yi masu wahala bisa wasu dalilai.
Kadan daga cikin dalilan kuwa kamar yanda wasu ke fadi shine suna yi ne don su wanzu kuma a zamto a karkashinsu a rika yi masu biyayya ko kuma a wanzu a biyayyar tasu.