So tari wasu lokuta Mutum yakan dawo abin ya dame sa ko har yaji ma ya kasa Barci ko ya rasa abin da yake yi mashi dad’i sakamakon wannan dukan da ya yiwa Yaro wanda kuma Yanzu bayan ya dawo hayyacinsa abin ya damesa yana ganin bai kamata ace wannan matakin ya ɗauka ba. To Lallai dama hakan na iya faruwa, abinda ya kamata mu fahimta anan shine kamar yanda masana ilimin halayyar ɗan Adam suka tabbatar kashi 90% na Duka bai zamto wa yana bada jawabi wurin Tarbiyya amma akwai lokutan da zai zamto Mutum ya yi dukan bayan bin matakan da su dace wanda basu bada natija ba to anan an yarda Mutum ya yi dukan amma shima bisa iya haddin da zai bada Ma’ana domin wannan dukan ba girman shi ko yawanshi ne ke bada jawabi ba a’a ana so ya zamto dukan ya fi daga zuciya ne ya shiga zuciya ta yanda Zai zamto lokacin lallai kayi ne domin Tarbiyyar tasa ba don ɗaukar fansa ko domin cutarwa ba sai kaga komai kankantar sa ya sanya yaron ya gane girman abinda ake so ya bari ko ya aikata.