Gulma Da Hanyoyin Kare Kai Daga Gare Ta Da Barin Ta | SHAFI’U & SHAIKH YUSUF JUDI

Share

GIBA DA MUMMUNAR ƘARSHEN MAI ITA. Malam YAyi mana cikakken bayani kan giba kamar yanda ya gabata sannan Yanzu zai ambato mana Illar da take sanya mai ita ana duniya da gobe kiyama. 1- Giba tana daya daga cikin alkaba’ir wato manyan laifuffukan da Allah ya ambace su a cikin Alkur’ani mai girma kuma wasu daga cikin su ma har ya ambaci irin azabar da Allah zai yi wa mai aikata bayan mutuwa da gobe kiyama. 2- Yana da ga irin munanan sakamakon da mai aikata GIBA ke fadawa Shine zai zamto bai da kima a cikin Mutane kuma baida kwarjini da mutunci a cikin al’umma baki ɗaya, kuma zai zamto kowa na gudunsa kuma bai son ya rabesa ko ya zama amininsa domin ya san zai iya fadin abubuwan da ba haka ba a bayan idon sa kuma abin da idannya ji bazai ji dad’i ba kuma kila bai tabbata yana da su ba wasu ma kila ya zamto tuhuma ne wanda shima yana daga cikin alkaba’iran da munanan ayyukan da Allah yake azabtar da masu aikata.

Wata mace da ta fuskanci wahalhalu tun daga haihuwarta – mahaifiyarta ta rasu, ta rayu cikin talauci, ta yi aikin bauta, aka tilasta mata aure, ta rasa mijinta, amma daga ƙarshe ta samu soyayya kafin ajalin mijinta.
Tasirin Zamantakewar Muharram | Shafi'u Haruna & Musa Muhammad Bello
Shafi'u Haruna da Musa Muhammad Bello suna tattaunawa game da mahimmancin ruhaniya a duniyar yau, bambancin ta da addini, da hanyoyin amfani da ita a rayuwa.