A wani taron manema labarai da ya gudana tsakanin fira ministan kasar Pakistan Mohammad shahbaz Sharif da Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi a yau litinin sun bayyana muhimmaci kasashen biyu su fadada dangantakar dake tsakaninsu musamman a bangaren tattalin arziki, siyasa kasuwanci da kuma al’adu dama sauran bangarori daban daban yadda zasu ci gajiyar juna.
Har ila yau shugaban kasar ya bayyana cewa batun yaki da ta’addanci tsakanin kasashen biyu lamari ne na hadin guiwa wa, domin mahangar kasashen guda biyu daya ne game da batun yaki da rashin tsaro da kungiyoyin dake fataucin miyagun kwayoyi
Ana sa bangaren pira ministan kasar ta Pakistan Shahbaz sharif ya bayyana cewa dukkan kasahen iran da Pakisatan sun damu matuka game da kasan gillan Gaza , kuma ya yi tir da HKi , kana ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta kawo karshen mamayar da Isra’ila ta yi wa yankin Gaza, kuma Pakistan za ta ci gaba da goyon bayan falasdinu ba tare da wani sharadi ba, kuma za ta ci gaba da hada kai da iran har sai an kafa kasar Falasdinu mai hedkwata a birnin Kudus