Zaben Iran: Wasu Karin mutane sun mika takardun neman tasayawa takarar shugabancin kasa

Wasu masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa a kasar Iran sun mika takardunsu, a rana ta biyar kuma ta karshe ta rajistar sunayen. ‘Yan takara

Wasu masu neman tsayawa takarar shugabancin kasa a kasar Iran sun mika takardunsu, a rana ta biyar kuma ta karshe ta rajistar sunayen.

‘Yan takara goma sha biyu da suka hada da wasu fitattun ‘yan siyasa ne suka gabatar da sunayensu a ranar Litinin.

Manyan ‘yan takarar da suka yi rajista a ranar litinin domin su tsaya takara su ne shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf da tsohon mataimakin shugaban kasa na farko Eshaq Jahangiri.

Da yake zantawa da manema labarai bayan rajistar, Qalibaf ya ce, manyan jami’ai na kasar ne suka yi kira gare shi da ya yi rijistar shiga takarar.

Shi ma  anasa bangaren tsohon mataimakin shugaban kasar Ishaq Janagiri ya shaida wa manema labarai cewa, ya yanke shawarar shiga takarar ne bisa fatan daukar matakin gyara hanyoyin da yake ganin ya kamata a yi gyara a kansu, da kuma samar da wasu sabbin dabaru na gudanarwa da kuma ci gaban kasar.

A ranar 28 ga watan Yuni ne za a gudanar da zaben gaggawa a Iran, inda za a zabi sabon shugaban kasar da zai maye gurbin marigayi shugaba Ibrahim Raisi, wanda ya rasu a mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin Iran a ranar 19 ga watan Mayu, tare da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, da wasu abokan huldar su shida.

Dole ne Majalisar kare kundin tsarin mulki ta tantance ‘yan  takarar kuma ta amince da su. Daga nan ne hukumar sa ido kan zaben kasar mai wakilai 12 za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 11 ga watan Yuni.

Wadanda hukumar tantance za su shafe makonni biyu suan yakin neman zabe, su gabatar da manufofinsu da kuma tsare-tsaren da suke da burin aiwatarwa idan har suka samu nasarar lashe zabe, kamar yadda kuma za su yi muhawara kai tsayea  gidan talabijin na kasa.

Daga cikin wadanda suka gabatar da sunayensu a baya-bayan nan dai domin tsayawa takarar shugabancin kasar ta Iran akwai tsohon shugaban kasar Mahmud Ahmadinejad, sai kuma tsohon shugaban majalisar dokoki Ali Larijani, da ma wasu daga cikin tsoffin jami’ai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments