Za A Gudanar Zaben Shugaban Kasa A Iran Zagaye Na Biyu A Mako Mai Zuwa

Zaben shugaban kasa a Iran ya koma zagaye na biyu, kuma daga yau Lahadi ne ‘yan takaran zasu fara yakin neman zabensu Hukumar zaben kasar

Zaben shugaban kasa a Iran ya koma zagaye na biyu, kuma daga yau Lahadi ne ‘yan takaran zasu fara yakin neman zabensu

Hukumar zaben kasar Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu tsakanin ‘yan takara Mas’ud Pezeshkian da Sa’id Jalili a ranar Juma’a mai zuwa. Kakakin kwamitin zaben Mohsen Islami ya ce adadin wadanda suka fito zaben a zangayen farko zasu kai kashi 40 cikin dari.

Zaben shugaban kasa a Iran ya doshi zagaye na biyu ne bayan rashin samun daya daga cikin ‘yan takarar da ya samun adadin kuri’un da ake bukata domin samun nasara a zagayen farko.

‘Yan takaran biyu, Mas’ud Pezeshkian da Sa’id Jalili, za su fafata a zagaye na biyu da aka shirya gudanarwa a ranar Juma’a mai zuwa, bayan da suka samu kaso mafi tsoka na kuri’un masu zabe, a cewar sanarwar da shugaban kwamitin zaben a ma’aikatar harkokin cikin gidan Iran ya fitar. Mohsen Islami.

Islami ya ce: Jimillar ra’ayoyin masu kada kuri’a sun haura sama da kuri’u miliyan 24 da dubu 535, kuma Pezeshkian ya samu kuri’u sama da miliyan 10 da dubu 400, yayin da dan takara mai rufa masa baya Jalili ya samu kuri’u miliyan 9 da dubu 400. Dan takara, Muhammad Baqir Qalibaf, ya zo na uku, inda ya samu kuri’u miliyan uku da 383,340, sannan dan takara, Mostafa Pourmohammadi, ya samu kuri’u 206,397.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments