Yemen Ta Jaddada Aniyarta Ta Mayar Da Martani Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Jinkirin mayar da martani daga ‘yan gwagwarmaya kan yahudawa lamari ne na dabarar yaki amma mayar

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Jinkirin mayar da martani daga ‘yan gwagwarmaya kan yahudawa lamari ne na dabarar yaki amma mayar da martanin ya zama dole.

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdul-Malik Badaruddeen al-Houthi, ya tabbatar da cewa: Mayar da martani ga hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan tankokin mai a tashar jiragen ruwa na Hodeidah na kasar Yemen, abu ne da babu makawa, yana mai nuni da cewa; jinkirin mayar da martanin batun ne na dabarar yaki da nufin neman cimma babban tasiri a kan abokan gaba.

A cikin jawabinsa game da ci gaban hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kaiwa Gaza da kuma ci gaban yankin, Sayyid Al-Houthi ya yi nuni da cewa: Jinkirin mayar da martani daga bangaren ‘yan gwagwarmaya gaba daya wajen dakile ta’addancin yahudawan sahayoniyya wani lamari ne na dabarar yaki kawai, da nufin samun damar mayar da martani mai gauni kan makiya domin koya musu babban darasi, yana mai jaddada cewa makiya yahudawan sahayoniya sun san babu makawa zasu fuskanci mayar da martani da kuma jaddada cewa babu ja da baya daga gare ta.

Sayyid ya kada da cewa: Babu wanda ya isa ya hana mayar da martanin ta hanyar barazana da tsoratarwa ko kuma matsin lamba, yana mai nuni da cewa; Akwai ci gaba da kokarin Amurka da Turai da wasu gwamnatocin kasashen Larabawa na dakile wannan martani, kamar yqadda har yanzu akwai hanyar sadarwa da sakonni da masu shiga Tsakani da suke neman Jamhuriyar Musulunci ta Iran da martaninta kan haramtacciyar kasar Isra’ila da kada ya kasance mai tsanani da rashin tasiri, yana mai nuni da cewa yunkurin tsoratarwa da yaudara suna fuskantar mayar da martani daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda lamarin ya shafi darajar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ce ta hanyar kashe bakonta kuma a babban birnin kasarta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments