Yemen: Sojojin Yemen Sun Kai Hari Akan Jirgin Ruwan Amurka A Tekun “Red Sea”

Kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari ya sanar da cewa; Sun kai hari akan jiragen ruwa biyu, daya na Amruka da kuma wani na HKI

Kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari ya sanar da cewa; Sun kai hari akan jiragen ruwa biyu, daya na Amruka da kuma wani na HKI a tekun India da kuma “Red Sea.”

Janar Yahya Sari ya kara da cewa, sun harba makamai masu linzami samfurin Ballistic 11 akan jirgin ruwan Amurka mai suna; “Olympic Sprit” wanda yake tafiya a tekun “Red Sea”.

Kakakin sojan na Yemen ya kuma ce, jirgin ruwa na biyu da su ka kai wa hari shi ne “ST. John” wanda yak e tafiya a tekun India, ta hanyar harba masa makami mai linzami samfurin “Cruise” .

Hare-haren da sojojin na Yemen su ka kai, suna a karkashin hana jiragen ruwa zuwa tasoshin ruwan HKI da suke yi, tun farkon yakin Gaza.

Janar Sari ya kuma ce; Za su cigaba da kai hari akan duk wani jirgin ruwa wanda yake nufar tashar jiragen ruwan HKI, har sai idan an kawo karshen yakin Gaza da kuma Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments