Yemen:  Sojoji Sun Kai Hari Da Jirgin Sama Maras Matuki Akan Birnin Tel Aviv NMa HKI

Sojojin Yemen su ka sanar da harba wani jirgin sama maras matuki zuwa birnin Tel Aviv na HKI, wanda ya yi barna ba tare da

Sojojin Yemen su ka sanar da harba wani jirgin sama maras matuki zuwa birnin Tel Aviv na HKI, wanda ya yi barna ba tare da an iya ganinsa balle kakkabo shi ba.

Kakakin sojojin Yemen, Janar Yahy Sari, ya sanar da cewa; sun yi amfani da sabon jirgin sama maras matuki wajen kai harin akan birnin Tel Aviv.

Wannan harin dai ya zo ne a daidai lokacin aka yi gagurumin gangami na nuna goyon bayan al’ummar Falasdinu a birnin  Sa’adah.

Al’ummar Kasar Yemen a birnin Sa’adah, sun yi gagrumin gangamin na nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu,inda su ka bayyana fushinsu akan cigaba da tafka laifukan HKI take yi akan al’ummar Gaza.

Mahalarta taron da sun kai miliyoyi a karkashin taken: “MUna Tare Da Mutanen Gaza, Ko Da Kuwa ‘Yan Kore Sun Ki.”

Tun fara kai wa  Gaza hari ne da HKI,al’ummar Yemen su ka shiga cikin sahun masu kai dauki ta hanyar hana jiragen ruwa zuwa HKI ta mashigar “Babal-Mandab”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments