Jaridar ta HKI ta bayyana cewa; Ana kara samun yawan sojojin da suke fuskantar matsalar kwakwalwa saboda dadewa a filin daga a Gaza da kuma Lebanon.
Jaridar ta kuma tabbatar da cewa; wasu sojojin 6 sun kashe kawukansu a cikin watanni kadan bayan dawowarsu daga yakin Gaza da kuma Lebanon.
Sai dai jaridar ta kara da cewa, wannan adadin na wadanda su ka kashe kawukan nasu, wani sashe ne kadan, domin sojojin kasar sun ki fitar da cikakken bayani akan adadin wadanda suka kashe kawukan nasu.
Wani sashe na rahoton ya kuma ce; Yanayi mai tsanani da sojojin suke shiga ne yake kidima su da yake kai su daukar rayukansu da kansu, kuma sai bayan kawo karshen yaki ne ma za a fahimci zurfin matsalar.
A gefe daya da akwai wasu sojojin masu yawa wadanda suke da bukatuwa da a kula da su a asibitin mahaukata na soja, saboda irin wadannan matsalolin da suke fuskanta.
A cikin makwanni kadan na bayan nan lamarin ya yi kamari ,musamman makwanni biyu na karshe, bayan lafawar yakin na Gaza da kuma baro fagen dagar Lebanon da wasu sojojin su ka yi.
Daga fara yakin zuwa yanzu, adadin sojojin HKI da su ka zama musakai sun 12,000 kamar yadda rahoton ya bayyana.