Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada A Gaza Tun Ranar 7 Ga Watan Octoban Shekara Ta 2023 Ya Kai 41,825

Yawan Falasdinawa wadanda HKI ta kai su ga shahada a zirin Gaza kimani shekara guda da ta gabata a yau ya kai mutum 41,825 da

Yawan Falasdinawa wadanda HKI ta kai su ga shahada a zirin Gaza kimani shekara guda da ta gabata a yau ya kai mutum 41,825 da kuma wasu 96,910 na wadanda suka ji raunin tun ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar kungiyar Hamas tana cewa a hare haren da sojojin HKI suka kai kan Falasdinawa a jiya Jumma’a sun kashe Falasdinawa 18 daga ciki har da daya daga cikin kwamdan ta a garin Tulkaram dake yankin yamma da kogin Jordan.  

A yau Asabar ma, a Gaza ya zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 12 a gaza kadai, 6 daga cikinsu a garin Nusairat daga arewacin zirin Gaza. Daya a Dair-Zur, 5 kuma a Beit-Hanoon .

Labarin ya kara da cewa wannan banda wasu kimani 10,000 wadanda suka bace ko kuma suke karkashin buraguzan gine ginen da aka rusa a kansa, wadanda kuma aka kasa fito da su. Labarain ya kara da cewa a garin Nusairat wani jirgin yakin HKI mai saukar ungulu ya yi ta barin wuta kan mai uwa da wabi a garin wanda ya kai mutane da dama suka kaiga shahada ko Rauni.

Amma a yankin yama da kogin Jordan sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa kimani 742 sannan 6,250 kuma suka ji rauni daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa yau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments