Yan Wasan Motsajiki Na Iran Sun Zama Zakara A Wasanin Motsa Jiki Na Yammacin Asia Karo Na 5

Yan wasan motsa jiki na kasar Iran sun zama zakara a gasar wasannin motsa jiki na kasashen yammacin Asia karo na 5 wanda aka gudanar

Yan wasan motsa jiki na kasar Iran sun zama zakara a gasar wasannin motsa jiki na kasashen yammacin Asia karo na 5 wanda aka gudanar a kasar Iraki.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta bayyana cewa yan wasannin motsa jiko na JMI  maza da mata, sun zama zakara ne tare da samun lambobin yabo har 40 wadanda suka hada da zinari 21 da kuma azurda 16 har’ila yau da tagulla 3.

Labarin ya kara da cewa,  kasashen Iraqi da Qatar ne suka zo na biyu da na uku tare da samun lambobin yabo 39 da kuma 12 a jare

An gudanar da wasannin motsa jikin na wannan shekarar ne a birnin Basra na kudancin kasar Iraki daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa -01 ga watan Yuki, kuma kasashen da suka sami halatar gasar sun hada da Iraki mai masaukin baki, Bahrain, JMI, Jordan, Kuwait, Lebanon, Oman, Falasdinu, Qatar, Saudia, Siriya , Hadaddiyar daulolin larabwa da kuma Yemen.

An gudanara wasannin motsa jikin ne har guda 48 a cikin kwanaki 4 da aka dauka ana gasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments