Rundunar ‘yan sandan kasar Faransa ta fara gudanar da bincike kan lamarin da ya faru na kona kofar Masallacin Al-Sunnah da ke kan titin Victorine Authier a yankin Amiens na kasar da gangan.
Tashr Farance 24 ta bayar da rahoton cewa, a safiyar Talata ne aka aike da jami’an kashe gobara zuwa wurin domin kashe wutar da ta tashi a kofar masallacin Al-Sunnah da ke birnin Amens. Gobarar dai ta tashi ne daga kofar masallacin kuma an gano wasu abubuwa da masu neman tsoka da tayar da hankalin musulmi suka bari a wurin.
Kofar masallacin Al-Sunnah ta baci saboda gobarar da aka tayar da gangan a wannan masallacin da ke kudu maso gabashin Amiens. Jami’an kashe gobara sun isa titin Victorine Authier da misalin karfe 6:00 na safe don kashe gobarar da ke gaban daya daga cikin kofofin ginin, a daidai lokacin da ‘Yan sandan suka isa wurin domin gudanar da bincike.
A cewar wata majiya da ke kusa da jami’an tsaro masu bincike, kuma an ga alamun wasu abubuwa masu cin wuta a wurin, amma dai babu wanda ya jikkata a wannan lamarin.
Kungiyar Al’adu da Addinin Musulunci ta AMCC mai kula da masallacin ta shigar da kara kuma a gaban kuliya, kuma tuni kotu ta bayar da umarnin fara bincike.
Abdulrahman Banghrin, sakataren kungiyar, ya yi imanin cewa da gangan aka yi wannan aikin, ya ce: “Wani ya banka ma wurin wuta, Muna ganin wannan hari ne a kan al’ummar Amiens, ba ma musulmi kawai ba.”
Ya kara da cewa: “Me ya sa a zahiri suka zabi wurin ibadar Musulmi?” “Ban sani ba kuma babu wanda ya sani, amma binciken ‘yan sanda zai fayyace wannan lamarin.”