‘Yan Sahayoniya Sun Yi Furuci Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi

Jaridar “Ha’arets” ta HKI ta buga wani rahoto da yake cewa, Fira minista Benjemine Netenyahu  tare da ministocinsa ne su ka bayar da umarnin a

Jaridar “Ha’arets” ta HKI ta buga wani rahoto da yake cewa, Fira minista Benjemine Netenyahu  tare da ministocinsa ne su ka bayar da umarnin a yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da kare dangi a Gaza.

Ita kuwa jaridar “Badiot Ahranot”  ta buga labarin da yake cewa: Sojoji suna son sauya fasalin yankin Gaza ne ta hanyar mayar da shi kashi uku. Jaridar ta cigaba da cewa, sojojin za su sauya wannan yankin ta hanyar sauya fasalin Kudanci Gaza da shi ne zai zama yanki na uku. Shi kuwa yankin arewacin Gaza din zai zama inda sojojin za su cigaba da zama a cikinsa na din din din.

A halin yanzu dai sojojin HKI suna kan ganiyar yi wa mazauna arewacin Gaza kisan kiyashi da rusa musu gidaje da zummar korarsu daga cikinsa. Har ila yau sojojin na mamaya suna amfani da yunwa a matsayin makami domin tilastawa Falasdinawa ficewa daga cikinsa.

Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi gargadin cewa, HKI tana yi wa Falasdinawan arewacin Gaza  horo da yunwa.

Ita kuwa hukumar agaji ta MDD dake kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira ta zargi ‘yan mamayar da cewa,suna yi wa Falasdinawa kisan kare dangi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments