A rana ta 287 da fara kai harin kan Gaza, an ji wani fashewa mai karfi tare da fadowar wani jirgin sama maras matuki ciki a birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila
Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun rawaito cewa: An ji fashewar wani abu mai karfi a birnin Tel Aviv da asubahin ranar Juma’a. Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta ce fashewar ta faru ne a kan titin Ben Yehuda da ke birnin Tel Aviv.
A cewar faifan bidiyo da ke aiki da shafin Intanet, fashewar ta faru ne sakamakon fadowar wani jirgin sama maras matuki ciki a kan titi a birnin Tel Aviv haramtacciyar kasar Isra’ila.
Hotunan bidiyo sun nuna tarwatsewar jirgin saman a kan wani titi, yayin da har yanzu mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila ba su ce komai ba kan lamarin tukuna.
An ji karar fashewar a yankuna da dama na Tel Aviv, kuma kafafen yada labaran yahudawan sahayoniyya sun bayyana cewa, ana gudanar da bincike domin sanin bayanan kan fashewar.
Wani mai magana da yawun ‘yan sandan haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Fashewar ta faru ne a daya daga cikin gine-ginen birnin na Tel Aviv, kuma jami’an tsaro sun isa wurin da fashewar ta auku domin shawo kan lamarin.