‘Yan Gwagwarmayar Iraki Suna Ci Gaba Da Kaddamar Da Hare-Hare Kan Yankunan Yahudawa

‘Yan gwagwarmayar Iraki sun kai hari kan sansanin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila a kwarin Jordan da tuddan Golan da aka mamaye ‘Yan gwagwarmayar kasar Iraki

‘Yan gwagwarmayar Iraki sun kai hari kan sansanin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila a kwarin Jordan da tuddan Golan da aka mamaye

‘Yan gwagwarmayar kasar Iraki sun sanar da cewa: Mayakanta sun yi ruwan bama-bamai kan wasu muhimman wurare na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin kwarin Jordan da kuma yankin tuddan Golan da suka mamaye a yammacin jiya Lahadi da wayewar garin yau Litinin, ta hanyar amfani da jiragen saman yaki marasa matuka ciki.

A cikin wata sanarwa da suka fitar sun jaddada cewa: A ci gaba da tunkarar ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya gami da jaddada goyon bayan al’ummar Falastinu da Lebanon, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da ‘yan ta’addan yahudawan sahayoniyya suka yi wa fararen hula da suka hada da yara da mata da tsoffi, Mujahidan kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Iraki sun kai wani muhimmin hari a kwarin Jordan da aka mamaye ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki, kuma sun nuna faifan yadda harin ya yi mummunan barna ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments