Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da adadin hasarar da makiya yahudawan sahayoniyya suka yi a hare-haren da ta kai musu
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Yawan hasarar da makiya yahudawan sahayoniyya suka yi, tun bayan fara wani abin da suka kira cewa “Atisayen sojin kasa a kudancin kasar Lebanon” ya yi sanadiyar halakar sojojin fiye da 100 tare da jikkata wasu 1,000 na daban da suka hada da manyan jami’an soji da kananan sojoji, baya ga tarwatsa tankokin yaki na Merkava 43, da na soja 8, da motocin Hummer guda biyu, da motocin masu sulke guda biyu, da na daukan sojoji da kakkabo jiragen saman marasa matuka ciki guda 4 kirar Hormuz 450, da kuma jiragen saman yaki kirar Hormuz guda biyu.
Ofishin gudanar da aikin gwagwarmayar kungiyar ta kasar Lebanon ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Makomar sojojin makiya yahudawan sahayoniyya na komawa zuwa mataki na biyu na “Atisayen sojin kasa” a kudancin Lebanon zai zame mafarki mai cike da takaici, musamman sakamakon ire-iren munanan hasarar da sukeci gaba da samu a fagage da dama.