‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Harba Makami Mai Linzami Kan Birnin Tel Aviv

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun harbi wani nau’in makami mai linzami zuwa birnin Tel Aviv da aka kasa kakkabo shi Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun harbi wani nau’in makami mai linzami zuwa birnin Tel Aviv da aka kasa kakkabo shi

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun kaddamar da wani hari na ban mamaki da nau’in makami mai linzami na M90 a jiya Lahadi kan birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma duk na’urorin da yahudawan sahayoniyya suka kafa domin kakkabo makamai masu liunzamisun gagara kakkabo makamin har ya isa inda aka saita shi, kuma harin ya zo ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka da’awar sun kawar da wani bangare mai yawa na karfin bangaren sojin  na kungiyar Hamas.

Wannan dai ba shi ne karon farko da dakarun Izzuddeen Al-Qassam ke kai hare-hare kan wuraren haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar amfani da wannan makami mai linzami ba, kamar yadda a baya suka yi amfani da shi a ayyukan da suka gabata kan ‘yan mamaya.

A karon farko dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun bayyana cewa: Sun mallaki ire-iren wadannan makamai masu linzami samfurin M90, a cikin watan Disambar shekara ta 2023, a gefen wani nazari da aka yi kan kayan aikin sojansu.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments