‘Yan Gwagwarmaya Na Iraki Sun Kai Hari A Sansanin ‘Yan Mamaya A Tuddan Gulan

Kungiyar gwgwarmayar ta Iraki ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa, ta kai wa manufofin HKI na soja hari a yankin tuddan

Kungiyar gwgwarmayar ta Iraki ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa, ta kai wa manufofin HKI na soja hari a yankin tuddan Gulan dake karkashin mamaya a matsayin mayar da martani ga kisan kiyashin da suke yi a Falasdinu da Lebanon.

Sanarwar ta kunshi cewa:

A karkashin cigaba da tafiya a tafarkinmu na gwagwarmaya da ‘yan mamaya, da kuma taimakon mutanenmu a Gaza Falasdinu da Lebanon, sannan kuma da mayar da martani akan kisan kiyashin da ‘yan mamaya masu kwacen kasa suke yi wa fararen hula, kananan yara da mata da tsofaffi, mayakanmu masu jihadin musulunci na Iraki, sun kai hari da safiyar yau Lahadi 13/10/2024 akan cibiyar soja ta ‘yan mamaya ta hanyar amfani da  jiragen yaki marasa matuki.

Gwgawarmayar musulunci tana sake jaddada cewa za ta cigaba da kai hare-hare akan sansanonin makiya cikin karfi.

Taimako daga Allah kadai yake zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments