‘Yan gwagwarmaya a Iraki sun gargadi Isra’ila kan shiga yaki da Lebanon

Kungiyar gwagwarmaya da kuma yaki da ta’addanci ta kasar Iraki ta yi gargadin cewa sabbin ka’idojin aikin za su yi wa Amurka da Isra’ila illa

Kungiyar gwagwarmaya da kuma yaki da ta’addanci ta kasar Iraki ta yi gargadin cewa sabbin ka’idojin aikin za su yi wa Amurka da Isra’ila illa matuka idan har gwamnatin yahudawan Isra’ila ta zabi kaddamar da farmaki kan kungiyar gwagwarmayar Hizbullah bisa zargin kai hari da makami mai linzami a tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye.

Kata’ib Hezbollah (Hizbullah Brigades) ta yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar yau Litinin, yayin da kafafen yada labarai na kasar Labanon suka bayar da rahoton wasu hare-hare da Isra’ila ta kai a wasu garuruwan da ke kudancin kasar Lebanon, a daidai lokacin da ake samun tashin hankali bayan harin da aka kai a garin Majdal Shams a tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye.

An samu rahotannin kai farmaki kan Hula, Markaba, Aita al-Shaab, Khiam, Shaheen, Yaroun, Meiss el-Jabal, Kfar Kila da Bourj al-Shamali da ke kudancin Lebanon.

“Idan har yahudawan sahyoniya suka yanke shawarar aikata wani abu na bude sabon yaki na gaba daya a Lebanon, tabbas za ta fuskanci martanni dab a ta tsammani, kamar yadda Amurka da ke mara baya ga Isra’ila kan ayyukanta na ta’addanci ita ma ba za ta tsira daga hare-haren martani ba, inji “Jaafar al-Husseini, kakakin kungiyar Kata’ib Hezbollah a Iraki.

Akalla mutane 12 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a ranar Asabar, a wani harin roka da aka kai a wani filin wasan kwallon kafa da ke garin Majdal Shams da ke tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye.

A cikin wata rubutacciyar sanarwar da ta fitar, Hezbollah ta ce, ba ta da alaka da lamarin, kuma ta musanta dukkan zarge-zargen karya game da hakan.”

Wasu rahotanni, a halin da ake ciki, sun ce mai yiwuwa fashewar ta samo asali ne sakamakon wani makami mai linzami da tsarin makaman kariya masu linzami na Isra’ila ya harba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments