Yahudawan Sahyuniya 8 ne suka halaka bayan saukar wani makamin Hizbullah a kansu

Tashar talabijin ta 13 ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, a wannan Alhamis yahudawan  sahyuniya 6 suka halaka a yankin  Metula da ke Upper

Tashar talabijin ta 13 ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, a wannan Alhamis yahudawan  sahyuniya 6 suka halaka a yankin  Metula da ke Upper al-Jalil, yayin da wasu biyu kuma suka halaka a yankin Kiryot, bayan wani harin roka da mayakan kungiyar Hizbullah suka kaddamar kai tsaye daga Lebanon.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun yi nuni da cewa, wasu makaman roka da aka harba daga kasar Lebanon sun afkawa taron sojojin Isra’ila a Metula, inda suka bayyana lamarin da cewa ya tsanata matuka. Rahotanni sun nuna cewa harin ya nuna yadda kungiyar Hizbullah ke ci gaba da kara tsanata hare-harenta a kan haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin lokutanan nan babu kakkautawa.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun kara jaddada cewa hare-haren da kungiyar Hizbullah ta kai a baya-bayan nan ya nuna cewa Hizbullah ta san inda za ta kai hari lokacin da take harba makamai a kan yankin Metula, wanda hakan ya haifar da mummunan sakamako ga sojojin Isra’ila.

 Bugu da kari, kafafen yada labaran yahudawa  sun nuna shakku kan cewa ko mazauna arewa za su iya komawa matsugunan su koda bayan kawo karshen yaki da Hizbullah.

Bayan afkuwar lamarin, mai magana da yawun sojin Isra’ila ya tabbatar da cewa an harba rokoki kusan 30 daga kasar Labanon, tsakanin karfe 12:21 zuwa 12:23 a yankunan tsakiya, da yammacin al-Jalil.

A wani labarin kuma, tashar 14 ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, rokoki sun kashe karin wasu yahudawan sahyuniya biyu tare da raunata wasu biyu a kusa da Kiryot a arewacin Falasdinu da Isra’ila ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments