Yahudawan Sahayoniyya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Neman Musayar Fursunoni Da Kungiyar Hamas

Yahudawa masu zanga-zanga sun tare hanyar zuwa ofishin Netanyahu domin neman kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da Falasdinawa Rahotonni sun bayyana cewa: Daruruwan yahudawan sahayoniyya masu

Yahudawa masu zanga-zanga sun tare hanyar zuwa ofishin Netanyahu domin neman kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da Falasdinawa

Rahotonni sun bayyana cewa: Daruruwan yahudawan sahayoniyya masu zanga-zanga sun tare hanyar zuwa ofishin Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ke yammacin birnin Qudus a jiya Talata, inda suka bukaci a gudanar da musayar fursunoni da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, sannan ‘yan sanda sun kama mutane bakwai daga cikin masu zanga-zangar.

Shafin yanar gizo na “Wala” na haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Masu zanga-zangar da suke neman canjin gwamnati a haramtacciyar kasar Isra’ila sun rufe hanyoyin zuwa ofishin Netanyahu tare da sanya akwatunan zabe a kan tituna don neman gudanar da zabe da wuri.

Kamar yadda masu zanga-zangar suka din ga rera taken neman gudanar da musayar fursunoni kafin ’yan sanda su tarwatsa masu zanga-zangar da karfi tare da kama bakwai daga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments