WHO: An Kawo Karshen Zazzabin “Malaria” A Kasar Masar

Hukumar Lafiya ta duniya  w.h.o ta bayyana Masar a matsayin kasar da ta kawo karshen zazzabin cizon sauro, tare da bayyana hakan a matsayin tarihi.

Hukumar Lafiya ta duniya  w.h.o ta bayyana Masar a matsayin kasar da ta kawo karshen zazzabin cizon sauro, tare da bayyana hakan a matsayin tarihi.

Kasar Masar ta yi dubban shekaru tana fama da zazzabin cizon sauro,amma yanzu ya zama tarihi kamar yadda shugaban hukumar lafiya ta duniya Dr. Tedros Adhanom ya bayyana.

Adhonam ya ce: Zazzabin cizon sauro, yana cikin cutuka da Masar ta yi fama da su a  lokaci mai tsawo na baya, amma yanzu ya zama tarihi.”

 Tun shekaru 100 da su ka gabata ne dai kasar ta Masar ta fara aiki tukuru domin ganin ta kawo karshen zazzabin cizon sauro a cikinta.

Sai idan kasa ta cika sharadin daukar shekaru uku a jere ba tare da an sami mutum daya da ya kamu da zazzabin cizon sauro ba ne ake shelanta kasa a matsayin wacce ta magance zazzabin.

A kowace shekara mutanen da su ka kai 600,000 ne wannan zazzabin yake kashewa,mafi yawancinsu a nahiyar Afirka.

Masar din ta zama kasa ta Farko a nahiyar da ma a duniya wacce ta kawo karshen zazzabin malaria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments