Wasu Matasa Sun Dawo Kan Tituna A Jihar Jigawa Bayan An Kafa Dokar Hana Fita

Duk tare da ‘dokar hana fita’ na sa’o’ii 24 a jihar Jigawa, wanda gwamnatin jihar ta kafa  wasu matasa sun fito kan tituna suna zanga

Duk tare da ‘dokar hana fita’ na sa’o’ii 24 a jihar Jigawa, wanda gwamnatin jihar ta kafa  wasu matasa sun fito kan tituna suna zanga zanga a wasu anguwanni a birnin Dutse babban birnin Jihar.

Jaridar Tribune ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta Jigawa ta kafa dokar hana fita na sa’o’i 24 bayan tashe tashen hankula da aka yi a rana ta farko na zanga zangar tsadar rayuwa. Amma a jiya jumma’a ma wasu daruruwan matasa a unguwar ‘wai’ na birnin dutse sun fito kan tituna.

Majiyar labarai daga birnin Dutse ya bayyana cewa a halin yanzu yansanda suna fafatawa da yaran da suka fito don ci gaba da zanga zangar tsadar rayuwa a kasar.

Wasu wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa yansanda suna fafatawa da wasu matasa a unguwar ‘Wai’ na birnin. Hakama a unguwar Shuwarin wasu masatan sun sake taruwa don ci gaba da zanga zanga.

Zanga zangar ranar daya ga watan Augusta dai ta yi sanadiyyar lalata dukiyoyi da dama a cikin birnin duste, da wasu wasu yankuna a jihar.  Labarin ya kara da cewa yansanda sun kama wasu matasa a mashigar garin Dutse, wasu daga cikinsu kananan yara ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments