Wall Street Journal:  Hizbullah Na Kara Kaimi Wajen Kai Hare-hare

Jaridar “ Wall Street Journal” ta kasar Amurka ta bayyana cewa; Har yanzu dakarun Hizbullah suna da karfin da za su iya jan Isra’ila

 Jaridar “ Wall Street Journal” ta kasar Amurka ta bayyana cewa; Har yanzu dakarun Hizbullah suna da karfin da za su iya jan Isra’ila cikin yaki na tsawon lokaci, duk kuwa da munanan hare-haren da ta kai wa kungiyar da kuma kashe jagororinta da ta yi.

Jaridar ta Amurka ta cigaba da cewa; Mayakan na Hizbullah suna yi wa sojojin Isra’ila kwanton bauna a kudancin kasar, haka nan kuma suna cigaba da kai hare-hare da jirage marasa matuki da kuma makamai masu linzami.

Dangane da shigar sojan kasa na HKI a kudancin Lebanon, jaridar ta “Wall Street Journal” manufar da Isra’ila take son cimmawa ita ce nesanta mayakan daga kan iyaka domin hana hare-haren da suke kai wa,,amma maimakon haka, mayakan kungiyar ne suke kara tsananta kai hare-hare.

Dangane da harin da Hizbullah ta kai da jirgi maras matuki wanda ya isa har dakin kwanar Fira minister Benjemine Netenyahu, jaidar ta ce; Shi ne karo na biyu da kungiyar ta tabbatar da cewa tana da karfin kutsa makaman tsaron sama na Isra’ila ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuki.

Wani sashe na rahoton jaridar ya kunshi cewa, yawan makamai masu linzamin da Hizbullah take  harba wa sun karu, ta yadda a rana daya tana iya harba makamai 200.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments