Wakilan Kasashen Duniya Sun Fice Daga Zauren Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Jawabin Netenyahu

Wakilan kasashe da dama na duniya ciki har da Iran, sun fice               daga cikin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya yayin jawabin fira ministan haramtacciyar kasar

Wakilan kasashe da dama na duniya ciki har da Iran, sun fice               daga cikin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya yayin jawabin fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu

Tawagogin kasashen Larabawa da na kasa da kasa da suka hada da tawagar Iran, sun fice daga cikin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, bayan da fira ministan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya haura kan mumbarin taron domin gabatar da jawabinsa a zaman taro karo na 79 na Majalisar Dinkin Duniya.

Yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta yada faifan bidiyo da ke nuna janyewar wakilan kasashen Larabawa da dama da suka hada da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Turkiyya, domin nuna rashin amincewarsu da kalaman Netanyahu da yake fuskantar zarge-zarge kan aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar Falasdinu a Zirin Gaza na Falasdinu.

Jami’an diflomasiyya a Majalisar Dinkin Duniya sun yi ta rera taken nuna adawa da fira ministan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, gabanin jawabinsa a Majalisar Dinkin Duniya, domin nuna adawa da ci gaba da cin zarafin bil’Adama a Gaza da Lebanon.

Idan dai ba a manta ba, Netanyahu na gabatar da jawabin nasa ne a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya Karim Khan ya bukaci a ba shi sammacin kama shi da ministan tsaronsa Yoav Galant har sau biyu, domin alhakinsu na aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments