UNRWA Ta Yi Allah-wadai Da Dokar Tilastawa Falasdinawa Yin Hijira Daga Khan Younis

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi Allah-wadai da sabon umurnin Isra’ila na kwashe  kimanin mutane 250,000 daga Khan

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi Allah-wadai da sabon umurnin Isra’ila na kwashe  kimanin mutane 250,000 daga Khan Younis a daidai lokacin da babu kusan wani yanki mai aminci a fadin Gaza”.

“Makonni kacal bayan da aka tilasta wa mutane komawa Khan Younis da ya lalace, hukumomin Isra’ila sun ba da sabon umarnin ficewa a yankin, “in ji hukumar a shafin ‘’X’’.

Rahotanni sun ce Jami’an lafiya da na gudanarwa sun fara kwashe marasa lafiya daga asibitin European Hospital da ke Gaza a birnin na Khan Younis gabanin yiwuwar Isra’ila ta sake kai farmaki yankin.

Jami’an sun fara kwashe marasa lafiya da wadanda suka ji rauni da kuma kayan aikin kula da lafiya saboda asibitin yana cikin yankin da mazaunansa suka samu sakonnin Isra’ila na su fice zuwa wani wajen.

Kusan watanni tara, yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga wuri zuwa wuri domin tsria da rayukansu a yankin da aka yiwa kawanya.

Umurnin janyewar Isra’ila na baya-bayan nan ya shafi ‘yan gudun hijira 250,000 a Khan Younis, birni na biyu mafi girma a Gaza, yayin da take kai sabbin hare-hare a kudancin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments