Turkiyya Ta Soke Duk Wata Yarjejeniyar Kasuwanci Da Isra’ila Saboda Yakin Gaza

Turkiyya ta dakatar da fitar da dukkan kayayyaki da kuma shigar da su Isra’ila, a wani mataki na nuna fishi game da yakin da Israila

Turkiyya ta dakatar da fitar da dukkan kayayyaki da kuma shigar da su Isra’ila, a wani mataki na nuna fishi game da yakin da Israila ke yi a Gaza.

“Turkiyya za ta aiwatar da wadannan sabbin matakai har sai gwamnatin Isra’ila ta bari an shiga da kayan agaji Gaza ba tare da katsalandan ba,” a cewar ma’aikatar cinikayya ta Turkiyya.

Sanarwar ta kara da cewa, “An aiwatar da mataki na biyu na wannan shiri, kuma an dakatar da fitar da kayayyaki zuwa Isra’ila da kuma shigo da su daga can”.

A watan jiya ne hukumomin Ankara suka sanya wa Isra’ila wasu tankunkuman kasuwanci, suna masu cewa ba za su dage su ba sai Isra’ila ta tsagaita wuta a yakin da take yi a Gaza tare da bari a shiga da kayayyakin agaji ba tare da shamaki ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments