Tsokacin Farko Na Shugaban Ofishin Siyasar Hamas Kan Kisan Gillar Da Aka Yi Wa ‘Yar Uwansa

Tsokacin farko da shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas ya yi bayan shahadar ‘yar uwarsa a wani kisan gilla da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi

Tsokacin farko da shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas ya yi bayan shahadar ‘yar uwarsa a wani kisan gilla da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi mata

Shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh ya tabbatar da cewa: Jinin ‘yar uwarsa Ummu Nahadh da ‘ya’yayenta da kuma jikokinta ya gauraya da jinin Falasdinawa a Zirin Gaza da yammacin gabar kogin Jordan da kuma duk wuraren da akwai al’ummar Falasdinu, kuma shahadarsu babu abin da zai kara masa, sai karfin gwiwa kan tsayin daka kan matsayinsu nagwagwarmaya da tabbacin ci gaba da tafiya a kan hanyar tare da samun tabbacin nasara.

Haniyeh ya kirga ‘yar uwarsa da iyalan gidanta a matsayin wadanda sukayi shahada, yana mai jaddada cewa: Sun samu daraja da matsayin shahada mai albarka da kuma shiga cikin yakin da zai yi nasara har abada.

Kungiyoyin gwagwarmaya a Falasdinu sun mika ta’aziyya ga Isma’il Haniyeh da dukkanin iyalan da ‘yan uwansu suka yi shahada ta hanyar kisan kiyashin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tare da goyon baya da kuma hannun Amurka da kasashen yammacin duniya, gami da Sanya albarkan gwamnatocin da suka kullar alakar jakadanci da yahudawan sahayoniyya, amma duk wannan mummunan halinsu ba zai taba karya karfin ruhi da azamar al’ummar Falasdinu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments