Tsohon shugaban CIA: Mummunan harin Isra’ila a Lebanon nau’i ne na ta’addanci

Tsohon sakataren tsaron Amurka kuma tsohon daraktan hukumar leken asiri ta CIA Leon Panetta ya bayyana cewa,  harin da Isra’ila ta kai a Lebanon da

Tsohon sakataren tsaron Amurka kuma tsohon daraktan hukumar leken asiri ta CIA Leon Panetta ya bayyana cewa,  harin da Isra’ila ta kai a Lebanon da ya hada da tarwatsa na’urorin sadarwa, hakan wani nau’i ne na ta’addanci.

“Ba na tsammanin akwai wata tambaya cewa wani nau’i ne na ta’addanci,” in ji Leon Panetta a wata hira da tashar CBS News ta kasarAmurka.

Tun kafin wannan lokacin dai Panetta yana da ra’ayin ganin cewa an yi amfani da hanyoyi na warware matsaloli ta hanyar lumana, maimakon yin amfani da tashin hankali da kashe-kashe kamar yadda Isra’ila take, wanda kuma ya sha bayyana haka a shekarun baya-bayan nan.

A ranakun Talata da laraba na makon da ya gabata ne dubban na’urorin sadarwa na Pagers da kuma na oba-oba suka tarwatse a Lebanon, wanda mafi yawa ‘yan kungiyar Hizbullah suke yin amfani da su.

Fashe-fashen sun faru ne a wuraren taruwar jama’a, inda mutane 39 suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma suka samu raunuka, da suka hada da mata da kananan yara.

Wani bincike na farko da hukumomin kasar Lebanon suka gudanar ya gano cewa an dasa wasu sanadarai maus fashewa a cikin na’urorin kafin su isa kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments