Tsohon Kwamandan IRIG Ya Ce: Yin Allawadai Kadai Kawai Ba Zai Dakatar Da Natanyahu Ba

Manjo Janar Mohsen Rizaei daya daga cikin kwamandoji dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC ya bayyana cewa gargadi da kuma

Manjo Janar Mohsen Rizaei daya daga cikin kwamandoji dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC ya bayyana cewa gargadi da kuma yin allawadai da da HKI ba zai sa Benyamin Natanyahu ya dakatar da abinda yake yi a kasashen Falasdinu da Lebanon ba.

Kamfanin dilldncin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Razae yana fadar haka a shafinsa ta twitter, a lokacinda yake bayyana alhininsa da hare-heren da HKI mafi muni a unguwar dahiya Junubiyya na birnin Beirut a jiya Jumma’a.

Raza`e ya bada shawara ga kasashen Iran, Iraqi, da Lebanon da su gaggauta daukar shawara  don  sanin yadda zasu kawo karshen yake yaken HKI a kasashen Falasdinu da Lebanon.

Manjo  Janar Razaei ya bayana cewa Natanyahu ba zai taba barin abinda yake yi ba, kuma idan har an barshi zai ci gaba da kai hare hare a kan biranen Bagdaza  da kuma Damascus bayan Beirut, sannan suna iya kawo hari birnin Tehran idan sunga damar yin hakan.

Daga karshe Manjo Janar Mohsen rizae ya ce ta bayyana a fil ikan cewa manya manyan kasashen duniya sun budewa Natanyahu damar ya ci gaba da abinda yake yi kamar yadda suka budewa Hitla a yakin duniya na II.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments